Old school Swatch Watches
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Tambayoyi Da Amsar su tare da
Sheikh Ibarheem Zakzaky na Arba'in da Uku


Sayyed Zakzaky2

TAMBAYA: Allah gafarta Malam, a yi mani karin bayani a kan gashin mage, wasu na cewa wai najasa ne? AMSA: Lallai ba haka ba ne. Illa iyaka dai wannan a babin kiwon lafiya, ba a babin fikihu ba, suna cewa yana sabbaba wani ciwo, kamar na tari, haka suke cewa. ..............

TAMBAYA: Allah gafarta Malam, a yi mani karin bayani a kan gashin mage, wasu na cewa wai najasa ne?

AMSA: Lallai ba haka ba ne. Illa iyaka dai wannan a babin kiwon lafiya, ba a babin fikihu ba, suna cewa yana sabbaba wani ciwo, kamar na tari, haka suke cewa. Saboda haka sukan guji ya fada a abinci. Amma a babin Fikihu, dahara, lallai ba najasa ne ba.

TAMBAYA: Allah kara wa Malam lafiya, ni bakanike ne, ko zan iya gyara motar coci?

AMSA: Eh, idan babu daukar kaskanci a ciki. Idan aikinsa ne kanikanci, kuma kowa yana kawo mota yana gyarawa har da na coci, ba laifi.

TAMBAYA: Allah ya kara wa Malam lafiya da kariya. Shin ko dan tireda zai iya fitar da humusi, kuma yaushe ya kamata ya fitar? AMSA: Shi khumusi ba ana sa ma mutum, ko a ce dan gari kaza ne, ko dan sana'a kaza ba. Akwai wani rara ne na dukiya da in ya kai yake zama khumusi ya hau kansa. Saboda haka sawa'un dan tireda ne shi, ko ma dan menene. Me yiwuwa kila a kan cinikin da yake yi na kasuwanci ne. Sai mu ce eh, khumusi na iya hawansa a ribar da ya samu, amma rarar riba da ya samu a kan cinikinsa.

TAMBAYA: Allah gafarta Malam, Ko wa za a ba khumusi?

AMSA: Zai bayar da shi ne ga Mujtahidi Fakihi wanda ya cika sharudda, ko Wakilinsa.

TAMBAYA: Akramakallahu, mutum ne ya sadaukar da sadakin diyarsa, wato shi zai biya sadakin sadaka, amma sai ya ki biya har lokaci mai tsawo. Ina matsayin wannan auren?

Daga Umar Yunusa Akafullah Jaji

AMSA: Lallai ba mu san wani abu wai shi sadaukar da sadaki ba. Abin da aka sani shi ne ana sa sadaki a biya. Wannan wani abu ne da mutane suka kirkira ma kansu, suna cewa wai sun sadaukar, har ma kuma ana ce ma diyar ma 'yar sadaka, wanda duk ba a san shi ba a shari'a. Amma abin da za mu dauka, shi wannan tun da shi ya dauka sadaki ya hau kansa ya biya sai bai biya ba, ya zama ana bin sa bashi ke nan. Amma in ya aurar da yarinyar ne a kan cewa ba sadaki, to ba ma auren.

TAMBAYA: Akramakallahu. Ina matsayin yin allura da rana a watan Ramadan?

Daga Yahaya Garba Gwamna Bunkure

AMSA: Ba laifi da shi.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, mutum ne zai yi tafiyar da ta isa kasaru a watan Ramadan, kafin ya bar gida sai ya ci abinci, sai bayan da ya fita, sai ya ji ashe ba a cin abinci sai an fara tafiya. Ina matsayin wannan azumin na wannan rana?

Daga Daga Yahaya Garba Gwamna Bunkure

AMSA: Lallai ya yi ganganci, don ya kamata mutum ya san hukuncin abu kafin ya aikata. Don ya ji an ce akan sha azumi in ana tafiya, to da sai ya tambaya, ya sharadin abubuwan suke? Don ba ma kawai sai zawwal ba, sai ma a tafiyar tasa ya kai haddin kasaru, in ya fita ma tafiyar, bai kai haddin da za a yi kasaru ba, lallai ma ba zai sha ba. Wato kamar yana cikin garin da zai yi tafiya din, bai riga ya fita ba, sai ya fita can bayan gari ya kai ma haddin kasaru, sannan yake iya sha. Saboda haka tunda ya yi wannan ganganci, za mu dauka bisa jahilci ne ya yi, wanda ya kamata za a yi la'akari da shi mutumin, Kaasiri ne shi, ko Mukassir. Wato wanda yana iya sani ne ya ki ya nemi ya sanin, ko kuwa ba zai yiwu ya sani ba ne; in ba zai yiwu ya sani ba ne, sai a ce ya rama, in kuwa zai yiwu ya sani ya ki sani, har kaffara sai ya yi.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Ina gaskiyar hadisin nan da ake cewa wai Manzon Allah (S) ya ce idan talauci ya damu mutum ya kara aure?

Daga Alkazim M. Alasan Kaduna

AMSA: To, ban san inda ya ga hadisin ba, kila yana ji ne a rediyo. Irin wadannan hadisan kuwa na rediyawa suna da yawan gaske, ba lalai ya zama Annabi ne ya fada ba, kamar wannan, ba a san Annabi ya fadi haka ba. Amma tana iya yiwuwa a cikin littafai masu kwashe-kwashe, wadanda ba su yi la'akari da ingancin abu ba, ya aka same shi. Amma gaskiyar magana shi ne, wannan bai inganta ba.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Daga wane lokaci ne hidimar 'ya'ya ke fadi daga kan iyayensu, wato daukar dawainiya?

Daga M. Alasan

AMSA: Wajibi ne mutum ya ciyar da 'ya'yansa da ba su balaga ba, amma ba za mu ce hidimar ta fadi ba ne, sai dai mu ce wajibcinsa. Zamansa dole, shi ne bai zama dole ba in sun balaga, amma ba ya fadi ba ne. Ka ga shi ya ce ya fadi ne, ka ga kuwa in abu ya riga fadi shi kenan yana nufin ba zai yi ba kenan. Amma wajibi, ya zama wujuban ya ciyar da 'ya'yansa wadanda na su balaga ba. Iyayensa kuma wadanda suka yi rauni, ya zama wajibi a kansa. Amma idan iyayen suna da wadata, ko kuma suna da karfinsu, bai hau kansa ba. Haka ma 'ya'ya, idan suka balaga, shi kenan bai hau kansa ba. Amma kalmar fadi, shi ne bai kamata ya fito ba a nan, sai dai a ce bai zama wajibi ba, amma ba ya fadi ba.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Maigidana ya ki biya wa yaranmu kudin makaranta, alhali yana da halin yin haka. Na yi masa magana, amma ya ki sauke nauyin da ke kansa. Allah gafarta ko zan iya fita, domin abin yana damu na?

AMSA: To, ban gane ma'anar fitan da ta ce ba. Kila tana nufin ta je ta nema kenan ko? Za ta iya fita nema, ita ta rinka biya tunda ita ta san muhimmancin karatun. Amma ba wanda zai ce mata a kan wannan ta fasa aure, tunda ai ma za ta jefa yaran cikin halin da ya ma ya fi wannan muni ne.

TAMBAYA: Mutum ne yana Kudancin kasar nan, sai abokan zamansa, Kiristoci suka kawo masa ambulan na neman gudummawa ga Cocinsu. Ko zan iya ba da gudummawata wajen gina Coci?

AMSA: To, ita takiyya, wanda ke cikinta yake sanin halin da yake ciki, in ba haka ba, ai shi ba abin da ya hada shi da gudummawar Coci, in dai ba ya zo a kan unwanin takiyya ne, ko da ma da ransa da mutuncinsa ba. Amma in ba haka ba, lallai bai kamata su tsammaci cewa musulmi zai ba su gudummawar gina Coci ba.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam idan iyaye suka doki yaronsu har suka ji masa rauni. Ko akwai wani hukunci da ya hau kansu?

AMSA: Eh, lallai za su biya diyya. Sai a yi kimar wanan raunin da suka ji ma 'ya'yan, sai su biya 'ya'yan. Da ma tun asali bai kamata a daki yaro a ji masa ciwo ba. Ya kamata in ya kai ma za a buge shi, to ya zamana an yanke masa hukunci ne a kotun gida, bayan an yi masa uzuri, kila ba laifin farko ne ba, ba na biyu ne ba, ba ma na uku ba ne, ya cancanci a yi masa bulala. To, sai a ce an yanke masa hukunci za a fyada masa rula a tafin hannu har sau uku, rular a kwance, ba a kaifin ba, karamar rula. In wata rana ya sake sai a yanke masa hukunci kila sau biyu. Har ma ina magana da yara, wata rana na ce, kila da hankici za a buge shi. Karo na biyu ne sai a ce da rula za a buge shi. Amma da ma ba ana dauko tsumagiya ba ne a dunga tsala ma yaro ko ta ko'ina ba, ba a yin haka nan. Ana yanke masa hukunci ne. Bulalar kuma ta kowane hali, kar ta kai goma, ko kuma in ce kada ya wuce goma.

TAMBAYA: Wa zai yi masu alkalanci?

AMSA: Shi a kansa yana iya ma kansa adalci. Sai ya kiyasta ya biya, ko ya sami wasu su yi masa kiyasi, sai ya biya. An ce Imam Khomaini ya taba biyo 'ya'yansa yana dan ba su tsoro kamar zai buge su, amma ba zai buga din ne ba, to sai daya ta fadi ta ji ciwo, sai ya sa aka yi kimanta, sai ya biya ta.

TAMBAYA: Yayan mahaifina yakan zagi mahaifiyarmu a gabanmu saboda Harkar Musulunci. Za mu iya mayar da abin ba komai ba, mu hakura, ko kuwa akwai matakin da za mu iya dauka?

AMSA: Abin da ya kamata, wannan su kai shi kotu ne a ladabtar da shi, don ba abin da ya hada shi da ita. Matar dan uwa ne, muharramarsa ce, kuma ita ajnaba ce a wurinsa, ba abin da ya hada shi da ita. Ko da a unwanin ladabi ba abin da ya hada shi da ita. Saboda haka ya kamata su kai shi kotu ne.

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din